While some people are doing anything possible to get fame, an actor, Umar Farouk, popularly known as Don Nas, cries out about how he is paying the price of fame in a way he didn’t expect.
A lokacin da wasu suke neman dauka ka a ta kowanne hali jarumi Umar Farouk, wanda aka fi sani da Don Nas, ya koka akan yadda yake biyan farashin daukaka a ta hanyar da bai zata ba.
00:30:33
source


























































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































Me ake son rubutawa a thumbnail ɗin? BAKA MAMA? ME WANNAN KE NUFI
In sai kun fara saka tallata za ku saki, to ku riƙa bambanta, a farkon na tallan sai ku sa.
Talla: Daukaka na…
Ko
Ɗanɗano: Ɗaukaka na…..
Idan za a saki kuma….
Cikakke: Daukaka….
Duk kuma da title iri ɗaya.
Mutum na gani zai san ga cikakken ga tallan, yana kuma budewa, shi kansa YouTube algorithm ɗin zai hanzarta turo masa bidiyon da ke da alaƙa da wanda ya buɗe saboda title din su yana da kamanceceniya.
Dan jarida
0:40 ina ma akwai timestamp/chapters akai
1:23 In an gama hira sai a kwanta a gado a huta 😂😂😂
1:42 Ba ku san amfanin su fara gabatar da tarihin su ko a taƙaice bane kafin a fara komai? Ku kanku idan sun gabatar za ku samu ƙarin tambayoyi da za su ƙarawa tattaunawar armashi
KUNA INA, 'YAN UWA?
1. Kubra mai wakar SARKIN FULANIN GOMBE NA GIDAN BUBA YERO…. Tana nan ita ma ko ta sheƙa? Akwai jita-jita mai yawa da ake yadawa kanta cewa tunda ta yi wakar matar sarkin Gomben ta kashe ta, wasu su ce mijinta ya tsine mata kafin ta yi wakar, da sauran labaran da har yanzu ba a tabbatar da gaskiyar su a kanta ba, saboda ba wata cikakkiyar hirar da aka yi da ita har yanzu a internet/social media platforms.
2. Yaushe za ku kawo wanda ya yi wakar FATI 'YAR ADAMAWA TUDUN YOLA, shi ma tunda ya yi wakar ta yi trending ya yi ɓatan dabo, yana raye ko ya mutu ba a sani ba.
3. Yaushe za a kawo hirar Prince Sulaiman Mai Sukus? Kamar yana raye kamar ba ya raye, saboda tun da waƙoƙin sa su yi trending a baya ba a sake jin sa ba.
4. Sunusi Anu, mai wakar Cakwala daɗi YARINYA DAGA NI SAI KE….. Shi ma yayi zamaninsa lokacin da ba Social media sosai. Yana ina yanzu? Ya aka daina jin labarin sa?
5. Waye yake da labarin A.Y FASHION wanda ya yi wakar KOMAI NA MATA NE IN KUN SAMU KU DINGA BA SU? Shi ma tun da ya yi wakar nan ta yi trending ba a sake sanin yana raye ko ya mutu ba. Yakamata ku gayyato shi domin tattaunawa mai zurfi da shi.
6. Sadiq Zazzaɓi, mai wakar YANZU ABUJA TA YI TSAF….. Ya shi ma ya yi shiru kamar ba ya raye?
7. Umar Mai Sanyi, me wakar NA CIKA BURINA IN NA GA RANAR AURENA, IN NA GAN NI A DAKINA BIYAYYA ZAN YI GA ANGONA. Shi ma ko hirarsa mai zurfi babu. Me yasa yanzu ba a jin shi ko a Kannywood? Ya yanzu ko sabbin wakokin sa babu?
8. Billy o, shi ma kamar ba ya raye yanzu?
9. Wa yake da labarin Altine Jibo, mai wakar MAMANA MAI ƘOSAI MAMANA MAI…. da WAYYO ALLAH MAMANA WAYYO ALLAH MAMANA.. da OWO OWO ƊAN ALEWA ƊAN ALMAJIRI MASU GAUGAWA da NI CE TA FARKO NI CE TA BAYA NI CE DANKALIN TURAWA…. Ko hirar ta a wata kafar watsa labarai babu yanzu haka, ina ta shiga ne? Ya aka ji ta shiru musamman a zamanin yanzu?
10. Hajiya Agwada Loko/Goggo Malka mai wakar A/E GWAGGO MALKA…. da A/E SOYAYYA…. CIKI DA GASKIYA WUKA BA ZA YA HUDA BA… Tun da ta bayyana ta samu daukaka amma yanzu shiru ake ji kamar ba ta raye, ita ma ba hirar ta ta musamman a internet/social media, me ya faru da ita? Ya a ji ta shiru?
11. Ina wanda ya rera wakar SO YANA DA DAƊI, MASO DASHIN WANI YA SHIGA HAUSHI, SOYAYYA TA ZAHIRI BA A YI MATA GUDUN BAREWA. Sunan sa MUSA PRECIOUS, shi ma wakarsa ta yi trending sosai a kasashen Hausawa a shekarun baya, har yanzu ana jin ta, amma ba bidiyon hirar sa, yana raye ko ya mutu ba wanda ya sani.
12. MARMAZA MARMAZA SOYAYYA KAUNA, A SOYAYYA, FUSKAR MASOYI DA HASKE…, Kamar AUWAL ADAM ne mawakin. Ku nemo sa a ji ina ya shiga shi ma?
Da sauran mutanen da su ma sun yi ɓatan dabo tun da su bayyana aka fara yayin su, sai aka daina jin su, ba labarin su, ba mai sanin suna raye sun bar harkar ne ko kuwa babu su a raye ne ba wanda ya sani. Ku zaƙulo su ku yi hira ta musamman da su, saboda su ma suna da nasu masoyan ko mabiyan da suke son sanin halin da suke ciki da sauran muhimman bayanai na rayuwar su.
Musamman su da su fara shahara lokacin da ba social media kamar yadda ake da ita a yanzu.
Sannan in ku gayyato celebrities, ku rinƙa tambayar su, wadanne ire-iren abubuwa ne su yi da su haifar da cecekuce a rayuwar su ko ya zama kalubale a harkar su, kuma ta ya su tsallake wadannan abubuwan. Ko kuma ku da kanku ku yi kokarin gano batutuwan sai ku tambaye su.
Title iri ɗaya ya dace ku riƙa yi a duk wani bidiyon da ya kasance mai talla da cikakke ne, saboda ta haka ne shi kansa YOUTUBE ALGORITHM zai gane tsarin bidiyon ta yadda ana bude Talla:… zai kawo Cikakke.. Saboda in bakwa haka za a samu matsala saboda bidiyoyin ku suna da tarin yawa kuma za ku cigaba da sako su ne, nan gaba kamar nan da shekaru 3 in mutum ya ci karo da talla ta ya zai gano sauran idan shi kansa algorithm bai gane wannan bidiyon yana da alaƙa da bidiyo kaza ba? In ko ya gane ga yanayin tsarin channel din shikenan.
Ga wata shawara da na ba wani channel da yake rarraba bidiyo, kamar za ta amfanar da ku kuma a yanzu ko anan gaba……
Ku zama kamar Usman Kabara mana daga full shikenan ba ƙari, shiyasa ma mutum yana ganin bidiyon ya san abinda zai gani, dan daga ya gama kalla ya san ba ƙari, in kuna cigaba da yayyanka shi nan gaba da bidiyoyi zasu yi yawa a tashar ku, za a samu matsala ta yadda ko mutum ya kalli wani yana son cigaban in ya duba ba zai ga full ba, kuma nan ba Tiktok bane bare a danna inda za a ga sauran.
Wannan tsarin naku bai ba dan ba tashar da take nuna kalar haka. Masamman in ya kasance maudu'i 1 ne kuma hira 1 ce sannan a channel 1.
Nan ba fa Gidan TV ko Rediyo bane, bare ku ce akwai jerin shirye-shirye, nan YouTube ne, duk shirin da ku sa shi za a gani, ba gidan TV bane bare ace ba lokaci sai an haɗu a wani makon.
Yaushe za ku fara kawo mawakan gargajiya?
Ya dace ku fara gayyato su daya bayan daya, musamman wadanda suka shahara, daga nan sai masu tasowa, da wa'yanda har yanzu ba su daina tafiyar ba.
In ku gayyato celebrities, ku rinƙa tambayar su, wadanne ire-iren abubuwa ne su yi da su haifar da cecekuce a rayuwar su ko ya zama kalubale a harkar su, kuma ta ya su tsallake wadannan abubuwan. Ko kuma ku da kanku ku yi kokarin gano batutuwan sai ku tambaye su.
Ga wata shawara da na ba Hadiza Gabon kila ta amfane ku……
Ki rika gayyato har shahararrun da wasunsu ma ake zaton kamar sun mutu babu su a raye. Wasu lokutan ma waɗanda aka daina jin labarin su su jama'a su fi ƙishirwar sanin halin da suke ciki ba waɗanda kusan duk wata tasha ko kafar watsa labarai akwai bayanan su akai ba.
PODCAST/TALK SHOW dai babban shiri ne a faɗin duniya, wanda yakamata ace zuwa yanzu kin sabunta shi ba sai 'yan Kannywood kadai ba.
Maimakon gutsura bidiyoyi ko rarraba shi, me zai hana a riƙa amfani da timestamp/chapter na YouTube, in ba ku san shi ba ku bincika shafin YouTube akwai cikakken bayani a kansa, saboda yin haka ya fi ma ɗaga darajar channel da bidiyon da a sa sama da rarraba shi.
Sannan a rinka amfani da Hausa Standard saboda ita ce Hausar da aka amince a yi amfani da ita a kafafen watsa labarai da makarantu, ita ce Hausar da kowa ke ganewa, ita ce a BBC, TRT, DW, RFI, VOA da littafan Hausa da sauran su, ba kuma Hausar Kano ce daidaitacciyar Hausa ba, idan ana son sani a tuntubi masana harshen Hausa, Hausar da ba a amince da ita ba ita ce kamar ta Kebbi,Sokoto, Zamata da sauransu saboda su dama ba sa cikin sahun Hausa Standard.
Sannan a riƙa zakulo zafafan tambayoyi ana jefawa bakon da aka gayyato ko bakuwar da aka gayyato, sannan ku fi karkata wurin tambayoyin da ba a cika yi musu su a sauran tattaunawar da aka yi da su ba, ba a rika maimaita tambayoyi iri guda koyaushe ba.
Sannan ana gayyato mutanen da ke tashe a entertainment industries kamar Fatima Hussain, Firdausi Yahaya, Salim Smart, Sadiq Saleh, Shamsiyya Sadi, Raba Gardama da sauransu.
Dan Allah ana kiyaye hakkin rubutun Hausa, gurin haɗa kalma a haɗa gurin rabawa a raba.
Idan wasu ne suke kula da shafin naku ya dace a ce an horar da su ka'idodin rubutun Hausa, duk wani yare yana da dokokin shi. Abin kunya ne a ce mutum yarensa ma bai san ka'idodin shi ba, ba abin takaicin ma kamar yadda na ga daidai da gurin title ma da kalmomin su ba yawa amma har yau jiya i yau.
Ki rinƙa gayyato masu tasowa har ma da duk wasu fitattun mutane na kowane fanni, rashin gayyato kowa ne yasa da aka ga hoton Malam Alkali Zaria aka yi caaaa a kanki.
In kin sabunta ki rinƙa gayyato manyan celebrities kamar yan siyasa, yan jarida, mawaka, yan tiktok, yan social Media, yan kwallon kafa, yan gwagwarmaya, yan dambe, mawakan gargajiya, mawakan zamani, marubuta, masana, malamai, shugabanni, jagorori, yan takara, yan kasuwa, yan soyayya, ma'aurata, likitoci, masu shirya finafinai, makaɗa, masu fassara finafinai, masu gabatar da shirye-shirye, masu zama a bayan kyamara , 'yan bariki, yammata da samari, ma'aikata, ɗalibai, sha'irai, malaman jami'o'i da sauransu. Ke har ma da duk wadanda za a iya samun darasi ko ilimi daga rayuwar su.
IDAN KI FADADA SHIRIN KI ZUWA KOWANE FANNI BA SAI KANNYWOOD KAƊAI BA, KE KANKI ZA KI SAMU DAMA TA TALLACE-TALLACE DA ƘARUWAR INCOME SOSAI DAMA DAMAMMAKI HAR A GWAMNATANCE DA SIYASANCE.
Sannan ki rinka basu damar faɗar tarihin su ko a takaice ne, da tambayar su gwagwarmayar su kafin su zama abinda su zama dan ba kowa ne ya sani ba.
Sannan ki ringa baiwa bako damar amayar da dik abinda ke ransa batare da kin katse masa hanzarin sa ba, wasu lokutan a haka ne za ki samu maganar da za ta sa bidiyon ya zama viral, wanda hakan kuma riba ce sosai a gurin ki. Katsewar ko zai sa firar ta ƙi daɗi har ma a rasa wasu batutuwan 😢
In hirar ku za ta kai sama da awanni 5 mai so zai kalla mara so kuwa koda minti 5 ne ba zai tsaya ya kalla ba.
Sannan matsalar ki ko ta masu kula da channel din naki basa danna alamar ❤ in an miki comments dan sa mabiyan ki su san kina ganin comments nasu.
Rashin haka illa ce babba, masamman wa ke da ki kasance babbar actress ce ke. Masamman wa comments da ya kasance na masoyan ki ko ya kasance mai amfani ba wanda ake zagi da cin mutunci a cikin sa ba.
Sannan muna bin ki bashin hirar Hamisu Breaker da sauran mawaka maza da mata .
Kodayake akwai banbanci tsakanin PODCAST da TALK SHOW amma dai kin fahimci shawarwarin nawa ai ko?
DUK MAI GOYON BAYAN WANNAN SHAWARA YA TOFA ALBARKACIN BAKINSA TA HANYAR REPLY KO DANNA ALAMAR LIKE ❤.❤❤
Gayyato manyan celebrities ne za su fi ɗaga darajar channel din ku, idan ku tara bidiyoyi na manyan celebrities to duk wani mutum da za ku yi hira da shi za ku samu masu kallo sosai, saboda a lokacin kun tara followers sosai da sosai.
Me yasa ba a gayyato manyan celebrities na Hausawa na wasu ƙasashen da ba Najeriya ba, kamar a Nijar akwai mawakan da ake kira Sogha a Sudan da Ghana da sauransu ma akwai su, in da dama mu fara ganin tattauanawar ku da su ba sai na nan gida Najeriya ba.
Ku samu ku gayyato Prince Daniel Aboki da Film ɗin sa na MAI MARTABA yanzu haka ya je matakin Oscar, akwai buƙatar ku yi tattaunawa mai zurfi da shi yanzu haka.
Yadda kuke kawo hira da yan films watau Entertainment industries da Music Industries, yakamata zuwa yanzu ace kun fara gayyato masana wannan abin suna sharhi da karin haske dan fayyace asalin abin nasu a ilimance domin ilmantar da su da ma al'umma gaba ɗaya. Kamar gayyato manyan malaman jami'o'i na fannin adabi da al'ada da masu sani sosai kan harkar entertainment industry da Music Industry a zamanance da hanyar raya ta da kalubalen da ke cikin ta da yadda za a iya amfani da ita domin samarwa matasa aikin yi da habbaka tattalin arzikin ƙasa.
In ku samu dama Dan Allah ku leƙa jihar Kaduna, ku gayyato Amina Amal, ku yi hira da ita domin tana da abubuwan da za ta ce kan zargin da ake mata kan wani bidiyo da Hadiza Gabon ta dinga cutar da ita, da takura ta ta amsa tambayoyin da take mata domin ta wanke kanta, alhalin a bayan fage har yanzu ana bayyana gaskiyar abinda ita Hadizan take ɓoyewa, hira da ita zai wanke ta daga zargin da ake mata, zai sa kuma a san uzurin ta, domin in za ku tattauna da ita ba dukan ta za ku yi ba ba marin ta za ku yi ba, saboda haka za ta samu yanci na bayyana cin zarafin ta da aka yi.
Ku samu ku yi tattaunawa mai zurfi da ita domin fito da abubuwan da ba a san su ba har ma da wadanda daidaikun jama'a suka sani. Ku cigaba da zama muryar waɗanda aka danne hakkokin su da muryar waɗanda suna da abinda za su ce amma ba su da hanyar da in sun gaya duk duniya za a ji.
Me yasa ba a kawo manyan Mawakan Baka na Gargajiya da na Zamani ana hira da su mai zurfi kan faduwa da nasarori da kalubale da yadda ma su fara tun a farkon farawa? Kamar kalar su Alhan Islam, Abba Yarima, Fauze Jantullu, Hidaya Mahmud etc
Ya dace ace zuwa yanzu kuna zakulo tsofaffin mawaka kamar su Ghali Money (Mai wakar Wasila kin ci amana ta), Musbahu M Ahmad (Mai wakar sangaya), Prince Sulaimanu (Mai wakar sojoji), Kabiru Yahaya (Kabiru Classic), Goggo Malka, Fati Musa (Rayuwa tana faruwa wucewa take…), Rabi Mustapha etc
Yakamata ace zuwa yanzu kun yi tattaunawa mai zurfi da Ya Amar da Anam
Ku rinka gayyato har mutanen da suke rubuta waka, ku tattauna da su a ji wakokin da su rubuta da har su shahara, da kuma me yasa su ba sa rerawa, da kalubalen su, da burin su na nan gaba.
Misalin su a yanzu Ibrahim Ibrahim ne, Kodayake shi yanzu yana rerawa.
Yaushe za ku gayyato Ɗangote, Mai Kamfanin BUA, A.A RANO etc?
Ku gayyato Aina'u Ade, akwai Magana a bakin ta, a kawo ta ai hira zazzafa da ita.
Ya har yanzu ba ku taɓa gayyato Aisha Baba Ahmad ba? Ko Saboda ba a ganin ta a Kannywood ne sai a Nollywood? Amma ai ta shahara ita ma a matsayin actress, Yakamata ku kawo ta ai hira mai zurfi da ita domin da alama za a ƙaru da ita.
Hirar ku tana kaɗan ku rinƙa yinta yadda Yakamata saboda akwai batutuwan da Yakamata ku rinƙa tambayar su amma duk ba ku tambayar su, sai ƙalilan daga ciki, tunda nan ba gidan rediyo bane bare ace akwai ƙarancin lokaci, to kuwa ya dace kuna musu tambayoyi yadda Yakamata tare fs da ba su damar su bayyana amsoshin su, da kuma tatsar su wajen samun ƙarin bayanan da suke son boyewa watau dai sai kun zama kamar gogaggun yan jarida.
Me yasa ba kwa gayyato mawakan zamani watau masu wakoki kalar na zamani? Kamar kalar su DJ AB, M SQUARE NAH, ERM BOI, Bilal Villah, Ngulde, Og Abbah etc
In ku gayyato celebrities, ku rinƙa tambayar su, wadanne ire-iren abubuwa ne su yi da su haifar da cecekuce a rayuwar su ko ya zama kalubale a harkar su, kuma ta ya su tsallake wadannan abubuwan. Ko kuma ku da kanku ku yi kokarin gano batutuwan sai ku tambaye su.
1:57 😂😂 KO ZA KA GAYYATO ME FADAWA KWATAR NE
2:11 Dan ma ba a ganin ka a manyan series, ko kai ne ka zaɓi iya Arewa24?