#HausaMovies #360Hausa #Hausafilms #Hausamovie #HausaFilm
#Latest Hausa Movies# #Adam A Zango# Latest Ali Nuhu Movies. #Latest Hadiza Gabon Movies. #Latest Rahama Sadau movies.#Latest Nafisat Abdullahi Movies. Click on the red button to subscribe to our YouTube channel for the best of Hausa Movies entertainment .
00:54:44
source











































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































































To, a ranar farko ta mako, Maryamu Magadaliya ta je kabarin da asuba, tun da sauran duhu, ta ga an kawar da dutsen daga kabarin. 2 Sai ta yiwo gudu wurin Bitrus da kuma almajirin nan da Yesu yake ƙauna, ta ce musu, “An ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuwa san inda aka sa shi ba.” 3 Sai Bitrus da almajirin nan suka fita suka doshi kabarin. 4Duka biyu suka ruga a guje, amma almajirin nan ya tsere wa Bitrus, ya riga isa kabarin. 5 Yana duƙawa yana leƙa ciki, sai ya ga likkafanin lilin a ajiye, amma fa bai shiga ba. 6Sa'an nan Bitrus ya zo a bayansa, ya kuwa shiga kabarin, ya ga likkafanin a ajiye, 7 mayanin kuma da yake kansa ba a ajiye tare da likkafanin yake ba, amma a naɗe shi kaɗai a waje ɗaya. 8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga, ya gani, ya kuma ba da gaskiya. 9 Don kafin lokacin nan ba su fahimci Nassin nan ba, cewa lalle ne yă tashi daga matattu. 10Sai almajiran suka koma gida.
Yesu Ya Bayyana ga Maryamu Magadaliya
(Mar 16.9-11)
11 Maryamu kuwa tana tsaye a bakin kabarin daga waje, tana kuka. Tana cikin kuka sai ta duƙa, ta leƙa kabarin, 12 sai ta ga mala'iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda dā gawar Yesu take, ɗaga wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu. 13 Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.” 14 Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ne ba. 15 Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.” 16 Yesu ya ce mata, “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” wato Malam. 17 Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.” 18 Sai Maryamu Magadaliya ta je ta ce wa almajiran, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma ce shi ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
Yesu Ya Bayyana ga Almajiransa
(Mat 28.16-20; Mar 16.14-18; Luka 24.36-49)
19 A ran nan da magariba, ranar farko ta mako, ƙofofin ɗakin da almajiran suke ciki na kulle don tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce musu, “Salama alaikun!” 20 Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da kwiɓinsa. Sai almajiran suka yi farin ciki da ganin Ubangiji. 21 Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama alaikun! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma na aike ku.” 22 Da ya faɗi haka ya busa musu numfashinsa, ya ce musu, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk waɗanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk waɗanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta ba ke nan.”
Rashin Bangaskiyar Toma
24 Toma kuwa, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ba ya nan tare da su sa'ad da Yesu ya zo. 25 Sai sauran almajiran suka ce masa, “Mun ga Ubangiji.” Amma ya ce musu, “In ban ga gurbin ƙusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsata a gurbin ƙusoshin, in kuma sa hannuna a kwiɓinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.”
26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama alaikun.” 27 Sa'an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsanka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.” 28Toma ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangijina Allahna kuma!” 29 Sai Yesu ya ce masa, “Wato saboda ka gan ni ka ba da gaskiya? Albarka tā tabbata ga waɗanda ba su gani ba, amma kuwa suka ba da gaskiya.”
Manufar Littafin Nan
30 Yesu ya yi waɗansu mu'ujizai da yawa dabam dabam a gaban almajiran, waɗanda ba a rubuta a littafin nan ba. 31 Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.
Sa'an nan Bilatus ya sa a tafi da Yesu, a yi masa bulala. 2Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura. 3 Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” suna ta marinsa. 4 Sai Bilatus ya sāke fitowa, ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi, domin ku san ban same shi da wani laifi ba.” 5 Sa'an nan Yesu ya fito, sāye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan jar garura. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin!” 6 Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.” 7 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Sharian nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.” 8Da Bilatus ya ji maganan nan sai ya ƙara tsorata. 9 Ya sāke shiga fāda, ya ce wa Yesu, “Daga ina kake?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10Saboda haka Bilatus ya ce masa, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka sani ba ni ne da ikon sakinka, ko gicciye ka?” 11 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.”
12 A kan wannan Bilatus ya nemi ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai, kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.” 13 Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna a kan gadon shari'a, wurin da ake kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata. 14 Ran nan kuwa ranar shirin Idin Ƙetarewa ce, wajen tsakiyar rana. Sai ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku!” 15Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu ba mu da sarki sai Kaisar.” 16 Sa'an nan ya bāshe shi gare su su gicciye shi.
An Gicciye Yesu
(Mat 27.32-44; Mar 15.21-32; Luka 23.26-43)
17 Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota. 18 Nan suka gicciye shi, da kuma waɗansu mutum biyu tare da shi, ɗaya ta kowane gefe, Yesu kuwa a tsakiya. 19 Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan gicciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.” 20 Yahudawa da yawa kuwa sun karanta wannan sanarwa, domin wurin da aka gicciye Yesu kusa da birni ne. An kuwa rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da kuma Helenanci. 21 Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce wa Bilatus, “Kada ka rubuta ‘Sarkin Yahudawa’, sai dai ka rubuta, ‘A faɗarsa shi ne Sarkin Yahudawa.’ ” 22Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta na rubuta ke nan.”
23Bayan soja sun gicciye Yesu, suka ɗibi tufafinsa, suka kasa kashi huɗu, kowane soja ya ɗauki kashi guda. Suka kuma ɗauki taguwa tasa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta. 24 Sai suka ce wa juna, “Kada mu tsaga ta, sai dai mu yi kuri'a a kanta, mu ga wanda zai ci.” Wannan kuwa domin a cika Nassi ne cewa,
“Sun raba tufafina a junansu.
Taguwata kuwa suka jefa kuria akanta”
25 Haka fa sojan suka yi. To, kusa da gicciyen Yesu kuwa da uwa tasa, da 'yar'uwa tata, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya, suna tsaye. 26 Da Yesu ya ga uwa tasa, da almajirin nan da yake ƙauna suna tsaye kusa, ya ce wa uwa tasa, “Iya, ga ɗanki nan!” 27Sa'an nan ya ce wa almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
Mutuwar Yesu
(Mat 27.45-56; Mar 15.33-41; Luka 23.44-49)
28 Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” 29 To, akwai wani gora cike da ruwan tsami a ajiye a nan. Sai suka jiƙa soso da ruwan tsamin, suka soka a sandan izob suka kai bakinsa. 30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa'an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.
An Soki Kwiɓin Yesu
31 Da yake ran nan ranar shiri ce, don kada a bar jikuna a gicciye ran Asabar (domin wannan Asabar ɗin babbar rana ce), sai Yahudawa suka roƙi Bilatus a karya ƙafafunsu, a kuma ɗauke jikunan. 32 Sai soja suka zo suka karya ƙafafun na farkon nan, da kuma na ɗayan da aka gicciye tare da shi. 33Amma da suka zo wurin Yesu, suka kuma ga ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. 34 Sai dai ɗaya daga cikin sojan nan ya soke shi da mashi a kwiɓi, nan da nan sai ga jini da ruwa suka gudano. 35 Wanda ya gani ɗin kuwa shi ya ba da shaida kan haka, shaida tasa kuwa gaskiya ce, ya kuma san gaskiya yake faɗa, domin ku ma ku ba da gaskiya. 36 Wannan kuwa don a cika Nassi ne cewa, “Ƙashinsa ɗaya ba za a karya ba.” 37 Wani Nassi kuma ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
Jana'izar Yesu
(Mat 27.57-61; Mar 15.42-47; Luka 23.50-56)
38Bayan haka Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izinin ɗauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izini, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu. 39 Nikodimu kuma, wanda farkon zuwansa wurin Yesu da dad dare ne, ya zo da mur da al'ul a gauraye, wajen awo ɗari. 40 Sai suka ɗauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lilin game da kayan ƙanshin nan, bisa ga al'adar Yahudawa ta jana'iza. 41A wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma da wani sabon kabari wanda ba a taɓa sa kowa ba. 42 Da yake ranar shiri ce ta Yahudawa, kabarin kuma na kusa, sai suka sa Yesu a nan.
Bayan Yesu ya yi maganan nan, ya fita, shi da almajiransa zuwa hayin Rafin Kidron, inda wani lambu yake, ya kuma shiga da almajiransa. 2 Yahuza ma wanda ya bāshe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba haɗuwa da almajiransa a can. 3 Yahuza kuwa bayan ya ɗauko ƙungiyar soja, da waɗansu dogaran Haikali daga manyan firistoci da Farisiyawa, suka zo wurin, riƙe da fitilu, da jiniyoyi, da makamai, 4 Yesu kuwa da ya san duk abin da zai same shi, ya yiwo gaba, ya ce musu, “Wa kuke nema?” 5Suka amsa masa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce musu, “Ni ne.” Yahuza kuwa da ya bāshe shi yana tsaye tare da su. 6Da Yesu ya ce musu, “Ni ne,” suka ja da baya da baya, har suka fāɗi. 7 Sai ya sāke tambayarsu, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.” 8Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku, ni ne. In kuwa ni kuke nema, ku bar waɗannan su tafi.” 9 Wannan kuwa domin a cika maganar da ya yi ne cewa, “A cikin waɗanda ka ba ni ban yar da ko ɗaya ba.” 10Bitrus kuwa da yake yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. Sunan bawan Malkus. 11 Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”
Yesu a Gaban Babban Firist
(Mat 26.57-58; Mar 14.53-54; Luka 22.54)
12 Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da dogaran nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi, 13 suka tafi da shi wurin Hanana da fari, don shi surukin Kayafa ne, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan. 14 Kayafa kuwa shi ne ya yi wa Yahudawa shawara, cewa ya fiye musu mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a.
Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu
(Mat 26.69-70; Mar 14.66-68; Luka 22.55-57)
15 Sai Bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajiri. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har gidan firist ɗin tare da Yesu, 16Bitrus kuwa ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai ɗaya almajirin da yake sananne ga babban firist ya fita, ya yi magana da wadda take jiran ƙofa, sa'an nan ya shigo da Bitrus. 17 Baranyar da yake jiran ƙofar kuwa ta ce wa Bitrus, “Anya! Kai ma ba cikin almajiran mutumin nan kake ba?” Ya ce, “A'a, ba na ciki.” 18 To, barori da dogaran Haikali kuwa sun hura wutar gawayi, don ana sanyi, suna tsaitsaye, suna jin wutar. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin wutar.
Babban Firist ya Tuhumi Yesu
(Mat 26.59-66; Mar 14.55-64; Luka 22.66-71)
19Sai babban firist ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwa tasa. 20 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba. 21Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.” 22 Da ya faɗi haka, wani daga cikin dogaran da suke tsaye kusa, ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?” 23 Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu to, ka ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, don me za ka mare ni?” 24 Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist.
Bitrus Ya Sāke Musun Sanin Yesu
(Mat 26.71-75; Mar 14.69-72; Luka 22.58-62)
25 To, Bitrus kuwa yana tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba cikin almajiransa kake ba?” Sai ya mūsu ya ce, “A'a, ba na ciki.” 26 Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dangin wanda Bitrus ya fille wa kunne, ya ce, “Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?” 27 Sai Bitrus ya sāke yin musu. Nan da nan kuwa zakara ya yi cara.
Yesu a Gaban Bilatus
(Mat 27.1-2, 11-14; Mar 15.1-5; Luka 23.1-5)
28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fādar mai mulki. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga fādar ba, wai don kada su ƙazantu su kāsa cin jibin Ƙetarewa. 29Saboda haka, Bilatus ya fito wajensu, ya ce, “Wace ƙara kuka kawo ta mutumin nan?” 30Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bāshe shi gare ka ba.” 31Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa a kan kowa.” 32 Wannan kuwa don a cika maganar da Yesu ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.
33 Sai Bilatus ya koma cikin fāda, ya kira Yesu ya ce masa, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” 34Yesu ya amsa ya ce, “Wato wannan faɗarka ce, ko kuwa waɗansu ne suka ce da ni haka a wurinka?” 35Bilatus ya amsa ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, jama'arku da manyan firistoci su ne suka bāshe ka gare ni. Me ka yi?” 36 Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaƙi kada a bāshe ni ga Yahudawa. Amma hakika, mulkina ba daga nan yake ba.” 37 Sai Bilatus ya ce masa, “Wato ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.” 38 Bilatus ya ce masa, “Wane abu ne, wai shi gaskiya?”
An Hukunta wa Yesu Mutuwa
(Mat 27.15-31; Mar 15.6-20; Luka 23.13-25)
Bayan da ya faɗi haka, ya sāke fitowa wurin Yahudawa, ya ce musu, “Ni kam, ban same shi da wani laifi ba. 39Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku mutum ɗaya. To, kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?” 40 Sai suka sāke ɗaukar kururuwa suna cewa, “A'a, ba wannan ba, sai dai Barabbas!” Barabbas ɗin nan kuwa ɗan fashi ne.
Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka, 2 tun da ka ba shi iko a kan dukkan 'yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3 Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko. 4 Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi. 5 Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni zuwa ga zatinka da ɗaukakan nan da nake da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance.
6 “Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka. 7Yanzu kuwa sun san duk iyakar abin da ka ba ni daga gare ka yake. 8 Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni. 9 Ni, roƙo nake yi dominsu. Ba duniya nake roƙa wa ba, sai dai su waɗanda ka ba ni, domin su naka ne. 10 Dukkan nawa naka ne, duk naka kuma nawa ne, an kuma ɗaukaka ni a zukatansu. 11 Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke. 12 Duk sa'ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kāre su, ba kuwa waninsu da ya halaka, sai dai halakakken nan, domin Nassi ya cika. 13 Amma yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu. 14 Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15 Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kāre su daga Mugun nan. 16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17 Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya. 18 Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya. 19Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.
20“Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙa wa ba, har ma masu gaskatawa da ni ta maganarsu, 21 domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa kai ne ka aiko ni. 22 Ɗaukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya, 23 ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane ka ƙaunace su kamar yadda ka kaunace ni. 24 Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba. 25 Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka , waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni. 26 Na sanar da su sunanka, zan kuma sana, domin ƙaunar da ka yi mini tă kasance cikinsu, ni ma in kasance a cikinsu.”
Masha Allah